Nigerian news All categories All tags
Tsadar mai: Hukumar DPR ta rufe gidajen mai 15 a wannan jihar

Tsadar mai: Hukumar DPR ta rufe gidajen mai 15 a wannan jihar

- Hukumar DPR ta rufe gidajen mai 15 a wannan jihar

- Gidajen man 15 a jihar Akwa ibom dake a kudu maso kudancin kasar nan suke

- Mista Tamunoiminabo Kingsley-Sundaye ne ya bayyana hakan

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin kayyade farashin man fetur a gidan man kasar nan watau Department of Petroleum Resources, DPR ta sanar da samun nasarar kunlle akalla gidajen mai 15 a jihar Akwa ibom dake a kudu maso kudancin kasar nan.

Tsadar mai: Hukumar DPR ta rufe gidajen mai 15 a wannan jihar

Tsadar mai: Hukumar DPR ta rufe gidajen mai 15 a wannan jihar

KU KARANTA: NNPC za ta gina matatar mai a Arewa

Hukumar dai ta bayyana cewa ta kulle gidajen man ne saboda sabawa umurnin kasa na saida mai a kan farashin da ya haura ma Naira 145 a jihar.

Legit.ng ta samu dai cewa babban Daraktan gudanarwar hukumar a jihar mai suna Mista Tamunoiminabo Kingsley-Sundaye ne ya bayyana hakan yayin da yake zagayawa da manema labarai a jihar domin duba yadda gidajen man ke aikin su.

A wani labarin kuma, Sahihan bayanan da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa rukunin kamfanonin nan mallakin gwamnatin tarayya dake kula da albarkatun man fetur watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) sun shiga yarjejeniya da gwamnatin jihar Kogi da zummar kafa matatar mai ta zamani watau biofuel plant a turance.

Kamar yadda muka samu, tuni har an kammala saka hannu akan takardar yarjejeniyar a garin Abuja, jiya Talata inda ake sa ran matatar man zata rika samar da mai domin ababen hawa nan ba da dadewa ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel