Nigerian news All categories All tags
Sace yan mata: PDP ta nemi Buhari ya tafi Dapchi

Sace yan mata: PDP ta nemi Buhari ya tafi Dapchi

- Babban jam’iyyar adawa ta kasa, PDP tayi raddi ga babban taron da APC ta gudanar a fadar Buhari

- Ta kuma nemi Buhari ya koma garin Dapchi

- Hakan ya biyo bayan sace yan mata daga wani makarantar Sakandare da Boko Haram suka yi

Rahotanni sun kawo cewa babban jam’iyyar adawa PDP ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tattara kayansa ya koma garin Dapchi domin ya gano mata 110 da aka yi amannar cewa kungiyar Boko Haram ta sace.

A wani jawabi daga mai magana da yawun jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa: "PDP na son Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da shakatawar da yake yi da jam'iyyar APC a fadar Aso Villa ya nuna yadda ake shugabanci ta hanyar tafiya Dapchi da ke Yobe, domin samun labari da zafinsakan abin da ya sa aka sace mata 'yan makaranta 110 yana ji yana gani".

Sace yan mata: PDP ta nemi Buhari ya tafi Dapchi

Sace yan mata: PDP ta nemi Buhari ya tafi Dapchi

Haka zalika PDP ta ce abin kunya ne ga shugaban kasar da jam'iyyarsa ta APC su rika biki da shirin zaben 2019 a fadarsa a lokacin da iyayen 'yan matan ke juyayin rashin ganin 'ya'yansu.

KU KARANTA KUMA: Zamu cika kasuwa da kananan kudi na naira – Inji CBN

A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka ta shigar da sunan jagoran wani tsagi na Boko Haram, Abu Musab Al-Barnawi cikin jerin gagga gaggan yan ta’addan da kasar ke sanyawa ido tare da nemansu ruwa a jallo.

Jaridar The Cables ta ruwaito ana zargin Abu Musa’ab Al-Barnawi da satar daliban kwalejin yan mata dake garin Dapchi na jihar Yobe a cikin satin daya gabata, wanda a shekarar da ta gabata ISIS ta sanar da shi a matsayin shugaban Boko Haram.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel