Nigerian news All categories All tags
Mashawartan shugaba Buhari na kawo koma baya a Najeriya

Mashawartan shugaba Buhari na kawo koma baya a Najeriya

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa na farko a Najeriya, Hassan A.Sommonu, ya bayyana cewa mashawartan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba su da ikon ciyar da ƙasar nan gaba sakamakon wasanni kawai da suke da siyasa da kuma rayukan al'umma.

Summonu ya bayyana hakan ne a yayin bikin murna na cikar kungiyar kwadago shekaru 40 da kafuwa, inda yace mashawartan shugaba Buhari suke kassara kasar nan da kuma al'ummar cikin ta.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Yake cewa, matakan da gwamnatin take dauka wajen tunkarar matsalolin kasar nan ba su da wani tasiri face ciyar da ita baya, inda ya nuna cewa mafi akasarin matsalolin tattalin arziki da tsaro suna afkuwa sakamakon rashin aikin yi da yayi kamari a kasar.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Ta'adin rikicin addini da ya afku a jihar Kaduna

Tsohon shugaban kungiyar ya bayar da misalin kamfanin karfe na Ajaokuta, da wasu mashawartan shugaban kasa ke yunkurin sayar da shi ga 'yan kasuwa a madadin gwamnati ta raya shi domin ciyar da kasar nan gaba.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani harin simame na mayakan Boko Haram ya salwantar da rayukan dakarun soji biyu a jihar Borno.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel