Mutane 4 sun jikkata yayin da aka gabza fada tsakanin makiyaya da manoma jihar Ebonyi

Mutane 4 sun jikkata yayin da aka gabza fada tsakanin makiyaya da manoma jihar Ebonyi

- Wani sabon rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya a garin Akaeze da ke karamar hukumar Ivo na jihar Ebonyi

- Rikicin ya yi sanadiyyar jikkatar manoma hudu da makiyaya hudu wanda a yanzu duk suna asibitoci inda suke karbar jinya

- Sakamakon rikicin, Gwamna David Umahi ya kafa dokar haramta kiwo a karamar hukumar ta Ivo har sai lokacin da kwamitin tsaro da ya kafa sun kammala binciken su kan musabbabin rikicin

Rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya a garin Akaeze da ke karamar hukumar Ivo na jihar Ebonyi a jiya, Sakamakon rikicin mutane hudu daga bangaren manoma da makiyaya duk sun sami munanan raunuka kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

Uku daga cikin makiyayan sun sami raunuka a kawunan su ne shi kuma daya daga cikin manoman ya sami raunuka saboda sarar da akayi masa a sassa daban-daban na jikin sa. An garzaya da manomin zuwa Asibitin koyarwa na tarayya da ke Abakaliki sauran makiyaya ukun kuma suna karban magani a wani asbiti a Awgu na jihae Enugu.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama mutane 18 kan rikicin addini na jihar Kaduna

Majiyar Legit.ng ta gano cewa makiyaya daga garin Mpu na jihar Enugu ne suka fadawa gonakin al'ummar Akaeze inda suka lalata musu amfanin gona, hakan kuma ya bata wa manoman rai inda ya fusata ya kai musu hari. Rahotani sun bayyana cewa mazauna garin sun fara ficewa don tsoron ramuwar gayya daga makiyayan.

Afkuwar lamarin ya tilasta Gwamna David Umahi na jihar ta Ebonyi daukan matakin haramta kiwo a karamar hukumar na Ivo har sai lokacin da aka kammala bincike kan musababin rikicin. Umahi ya kira taron gagawa na tsaro inda ya gayyaci shuwagabanin makiyaya, ciyamomin kananan hukumomi, shugabanin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

A baya, Legit.ng ta kawo wani rahoto inda Gwamna David Umahi ya kafa dokar hukuncin zaman yari na shekaru biyar ga duk manomin da ya kashe shanu ko kuma makiyayin da ya barnata amfanin noma a gonar makiyayan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel