Nigerian news All categories All tags
Kwastam ta kwace motoci 177 iyakar Legas

Kwastam ta kwace motoci 177 iyakar Legas

- Hukumar kwastan reshen zone 1 dake Ikeja ta kwace motoci 177 a iyakar Legas

- Tawagar majalissar dattawa ta ziyarci Legas dan gudanar da bincike akan kayan da kwastam ta kwace

Hukumar Fasa kwabri na Najeriya ta kwace motoci 177 da haramtattun kayan abinci daga hanun ‘yan sumoga a iyakar Legas a ranar Talaa.

Kwantrolla Janar na Zone A, reshen Ikeja jihar Legas, Mohammed Garba, ya bayyana haka a lokacin da tawagar kwamitin majalissar dattawa dake kula da al’amarin kwastam ta ziyarci yankin, dan bibiyar ayyukan su.

Kwastam ta kwace motoci 177 iyakar Legas

Kwastam ta kwace motoci 177 iyakar Legas

Shugaban kwamitin, Hope Uzodinma, ya jagoranci tawagar zuwa Legas.

KU KARANTA : Kurungus! Uwar jam’iyyar APC ta rabar gardama game da rikicin shugabancin APC a Kaduna

Mohammed Garba, ya ce za a kai kayan da suka kwace zuwa kotu dan a yanke hukunci akan abun da za ayi da su.

“Kotu ta kan mallakawa gwamnatin tarayya kayan da muka kwace saboda a baje kolin su,” Inji Mohammed Garba

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel