Nigerian news All categories All tags
An gurfanar da 'dan tsohon gwamna gaban kotu bisa almundahanar biliyan N1.5bn

An gurfanar da 'dan tsohon gwamna gaban kotu bisa almundahanar biliyan N1.5bn

- Nanle Miracle, dan tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, ya gurfana gaban kotu bisa tuhumar sa da almundahanar kudi biliyan N1.5bn

- An gurfanar da shi gaban shari'a Ijeoma Ojukwu na kotun tarayya dake Abuja

- An garkame shi a gidan yari har zuwa lokacin da kotun zata saurari kudirin belin sa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da Nanle Miracle, dan tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, bisa wasu caji guda shida da su ka hada da safarar kudi da yawansu ya kai naira biliyan 1 .5 ta hanyar amfani da daya daga cikin bankunan dake kasar nan.

Badakalar N1.5bn: An gurfanar da 'dan Gwamna Joshua Dariye a gaban kuliya

Badakalar N1.5bn: An gurfanar da 'dan Gwamna Joshua Dariye a gaban kuliya

An gurfanar da Miracle tare da Otel din 'Apartment le Paradis' inda yake aiki a matsayin Direkta a gaban Justis Ojukwu Ijeoma na babban Kotun Tarayya da ke Abuja.

KU KARANTA: Kwastam sun kama motoci 18 da buhunan shinkafa sama da 4000 a watan Fabrairu

Hukumar ta EFCC ta bayyan cewa wanda ake tuhuma ya ki sanar da hukuma lokacin da aka tura masa kudi sama da naira miliyan 10 zuwa asusun ajiyar bankin Otel din wanda hakan ya sabawa doka.

Hakazalika, Ba'ayi wa Otel din rajista da hukumar DNFI ba wanda hakan ya ci karo da sashi na 5(1) da 5(b) na dokar hana ta'annati da kudi na 2011.

Legit.ng ta gano cewa wanda ake zargi ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa dashi kuma lauyan sa Charles Abalaka ya roki kotu da bayar da belin Miracle duk da cewa bai gama shirya takardan izinin neman belin ba tare da gabatar da mutane biyu da zasu tsaya ma wanda ake tuhuma.

Alkalin kotun Justice Ojukwu ya amince da bayar da belin kan kudi naira miliyan 5 tare da masu tsaya masu mutum biyu duk mazauna birnin Abuja. Wanda ake yuhumar kuma ya mika wa kotu fasfo din sa da takardan mallakar filaye kafin lokacin da za'a fara sauraron karar na sa a 1ranar 10 da 12 ga watan Afrilu na 2018.

Alkalin kotun ya kara da cewa wanda ake tuhumar zai kasance a hannun hukumar EFCC har zuwa lokacin da lauyan sa ya kammala rubuta izinin neman belin nasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel