Charly Boy da sauransu sunyi zanga zanga a hedkwatar NNPC kan karancin man fetur

Charly Boy da sauransu sunyi zanga zanga a hedkwatar NNPC kan karancin man fetur

- Gamayyar kungiyar nan ta Our Mumu Don Do sunyi zanga-zanga a hedkwatar NNPC

- Charles Oputa wanda aka fi sani da Charly boy shine ya jagoranci zanga-zangar

- Kungiyar yan kasuwan mai wato DAPMAN ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 na biyan bashin N650bn da ma’aikata ke bin ta

Charles Oputa wanda aka fi sani da Charly da wasu yan zanga-zanga sun mamaye hedkwatar kamfanin man fetur din Najeriya (NNPC) domin yin zanga-zanga kan karancin man fetur da yaki ci yaki cinyewa a kasar.

Jaridar Sun ta ruwaito cewa an gano masu zanga-zangan karkashin kungiyar Our Mumu Don Do suna wake-wake a hedkwatar na NNPC a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu kan wahalar da yan Najeriya ke fuskanta saboda rashin mai.

Charly Boy da sauransu sunyi zanga zanga a hedkwatar NNPC kan karancin man fetur

Charly Boy da sauransu sunyi zanga zanga a hedkwatar NNPC kan karancin man fetur

A halin da ake ciki a ranan Talata, kungiyar yan kasuwan mai wato DAPMAN ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 na biyan bashin N650bn da ma’aikata ke bin ta.

KU KARANTA KUMA: Minista Dambazzau na ganawa da Sufeto Janar, da kuma manyan jami'an yan sanda (hotuna)

Duk da cewa kamfanin NNPC ke shigo da man fetur yanzu, NNPC ba tada Depot na ajiyan mai na kanta, innama ta dogara da wadannan yan kasuwa ne.

A wani jawabin da sakataren kungiyar, Olufemi Aewole, ya saki, DAPPMAN ta ce idan har gwamnati bata biya kudaden nan ba kafin mako biyu, zata wajabtawa ma’aikatanta suk shiga yajin aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel