Minista Dambazzau na ganawa da Sufeto Janar, da kuma manyan jami'an yan sanda (hotuna)

Minista Dambazzau na ganawa da Sufeto Janar, da kuma manyan jami'an yan sanda (hotuna)

Ministan dake kula da harkokin cikin gida, Abdulrahman Danbazau, na cikin ganawa da sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris da kuma manyan jami’an rundunar a hedkwatar hukumar tsaro.

Koda dai ba a kawo cikakken bayanin ganawar ba, Daily Sun ta ruwaito cewa kudirin ganawar na iya samun nasaba da kudirin kama makamai da basa ka’ida wanda Idris yace ya zamo abin tsoro a kasar.

An samu labarin cewa Idris yace yana da matukar muhimmanci a kwace makamai daga hannayen da basu dace ba a kasar musamman a daidai lokaci da zabe ke gabatowa.

KU KARANTA KUMA: Yusuf Buhari na nan da ransa, ku daina yada labaran karya - Onochie

A baya Legit.ng ta rahoto cewa anar Alhamis din da ta gabata ne wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, suka kai hari kauyen Birane dake cikin karamar hukumar Zurmi, a jihar Zamfara, inda suka kashe sama da mutune arba'in.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel