Ba zamu bari jam'iyyar APC ta sukurkuce ba - Akande

Ba zamu bari jam'iyyar APC ta sukurkuce ba - Akande

Tsohon shugaba mai rikon kwarya na jam'iyyar APC, Cif Adebisi Akande, ya yi kira ga mambobin jam'iyyar akan su goyi bayan jagorancin tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, wajen tabbatar da sulhu a cikin ta.

A raar Talatar da ta gabata, jigon na jam'iyyar ta APC ya yi wannan kira a yayin ganawa da manema labarai a birnin Osogbo na jihar Osun, inda yake cewa ba za su bari jam'iyyar ta daidaice ba.

Bisi Akande tare da Tinubu yayin ziyarar shugaban kasa a fadar sa

Bisi Akande tare da Tinubu yayin ziyarar shugaban kasa a fadar sa

A sakamakon gabatowar zaben kasa na 2019, akwai rashin jituwa dake ci gaba da yaduwa a tsakanin wasu mambobin jam'iyyar, inda har aka samu wariya da wasu fusatattun jam'iyyar suka kafa kungiya a garin Kaduna cikin makon da ya gabata.

KARANTA KUMA: 'Yan majalisar dattawa 10 da basu amince da sauya jadawalin zabe ba

Domin ganin wannan rikicin na cikin gida bai kawo tangarda a jam'iyyar ba a yayin gudanar da zabe, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi Tinubu akan ya zamto kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar da zai kawo sulhu a tsakanin mambobin ta.

A yayin haka kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an cafke 'yan ta'adda 4 da laifin kisan wani jigo na jam'iyyar PDP a jihar Ribas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel