IGP Idris: Zaman lafiya ya fara dawowa jihar Benuwe

IGP Idris: Zaman lafiya ya fara dawowa jihar Benuwe

- IGP Ibrahim Idirs yayi taro akan zaman lafiya da dattawan jihar Benuwe da Nasarawa a ranar Talata

- Shugaban 'yansandan Najeriya yace zaman lafiya ya fara dawowa jihar Benuwe

Sfeto janar na ‘yansanda, Ibrahim Idris, yace zaman lafiya ya fara dawowa jihar Benuwe.

Idris ya bayyana haka ne a taron zaman lafiya da masu ruwa da tsaki a jihar Benuwe da Nasarawa suka gudanar a birnin Abuja a ranar Talata.

Wannan shine karo na biyu da shugaban ‘yansandan Najeriya ke halartar irin wannan taro saboda shawo kan matsalolin tsaro da jihohin ke fuskanta.

IGP Idris : Zaman lafiya ya fara dawowa jihar Benuwe

IGP Idris : Zaman lafiya ya fara dawowa jihar Benuwe

Taro na farko da suka gudanar a watan Janairu bai haifar da da mai ido ba saboda duka gwamnonin jihohin ba su halarci taron ba.

KU KARANTA : Adadin kananan yaran dake fama da yunwa a Najeriya ya Karu

Mataimakin gwamnan jihar Benuwe, Benson Abuonu ya jagoranci tawagar jihar Benwue zuwa taron sai kuma mai ba wa gwamnan jihar Nasarawa shawara a fannin tsaro Dr. Muhammad Adeka ya jagorancin tawagar jihar Nasarawa zuwa taron.

Ibrahim ya ce a anyi taron ne da samar da zaman lafiya na tsawon lokaci a jihohin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel