Malamin makaranta ya fyade daliba mai shekaru 10, ya saka mata cututtuka

Malamin makaranta ya fyade daliba mai shekaru 10, ya saka mata cututtuka

- Malami mai shekaru 31 ya yiwa dalibar sa mai shekaru 10 kacal a duniya fyade

- Kotu ta bayar da umarnin garkame malamin, David Eyo, a gidan yari

- Binciken likitoci ya tabbatar da cewar yarinyar ta kamu da cututtuka masu yaduwa ta hanyar jima'i

Wani malamin makaranta, David Eyo, ya yiwa dalibar sa mai shekaru 10 fyade.

Yanzu haka wata kotu a jihar Legas ta bayar da umarnin garkame malamin, mazaunin unguwar Surelere, a gidan yari.

Malamin makaranta ya fyade daliba mai shekaru 10, ya saka mata cututtuka

Malamin makaranta ya fyade daliba mai shekaru 10, ya saka mata cututtuka

Alkaliyar kotun majistaren, B. O. Osunsami, ta yi umarnin a yi kwafin takardar karar a aika sashen gurfanarwa na jihar Legas domin su bayar da shawarar abinda ya dace kotun ta yi a kan mai laifin.

DUBA WANNAN: Na'urorin tsegumi a jihar Legas sun tona asirin wasu batagari

Dan sanda mai gabatar da kara, Benson Emuerhi, ya shaidawa kotu cewar wanda ake zargin ya aikata laifin ne ranar 10 ga watan Fabrairu a harabar makarantar dake gini mai lamba 17 a kan titin Aminu Junaidu, unguwar Surelere, jihar Legas.

Binciken likitoci ya tabbatar da cewar yarinyar ta kamu da cututtuka masu yaduwa ta hanyar jima'i.

Kotu ta daga sauraron karar ya zuwa ranar 25 ga watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel