Kwanan makiyaya masu kashe mutane ya kare - Buratai

Kwanan makiyaya masu kashe mutane ya kare - Buratai

Babban hafsan sojin tarayya, Laftanan Janar Tukur Y Buratai ya alanta fito-na-fito da makiyaya masu kashe mutane.

Ya ce irin hare-haren da suke kaiwa ya kori manoma 25,000 daga muhallansu a jihar Nasarawa kadai.

Babban hafsan sojin tarayya ya bayyana hakan ne a garin Lafiya yayinda ya kai ziyara ga gwamnan jihar, Umar Tanko Al-Makura.

Ya ce jami’an soji sun gano hanyoyin da makiyayan ke amfani da shi wajen kai hare-hare a iyakan Nasarawa da Benuwe kuma an tura jami’an soji wuraren.

Yace atasa’in tseren mazuru da aka kaddamar a jihar Benue zai shigo jihar Nasarawa kuma ya bada tabbacin cewa cikin makonni 6 kacal, komai zai dawo daidai.

Kwanan makiyaya masu kashe mutane ya kare - Buratai

Kwanan makiyaya masu kashe mutane ya kare - Buratai

Gwamnan jihar, Tanko AlMakura ya ce zuwan jami’an soji ya yi matukar taimakawa wajen kawo zaman lafiya jihar.

Ya yi alkawarin cewa zai baiwa jami’an tsaro dukkan gudunmunwan da suke bukata wajen kawo karshen makiyaya da kuma tabbatar da cewa wadanda aka kora daga muhallasu sun koma.

KU KARANTA: INEC, hukumomin zabe na jiha, zasu gana a kan zaben kananan yara

A karshe, gwamna Al-Makura ya baiwa hukumar soji N200 miliyan domin karasa barikin hukumar soji da ke karamar hukumar Doma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel