An cafke mutane 4 da laifin kisan wani jigo na jam'iyyar PDP a jihar Ribas

An cafke mutane 4 da laifin kisan wani jigo na jam'iyyar PDP a jihar Ribas

Cikin 'yan ta'adda biyar da suka salwantar da rayuwar wani jigo na jam'iyyar PDP a jihar Ribas, Heaven Ihuigwe, hudu daga cikin sun shiga hannun jami'an tsaro na 'yan sanda na birnin Fatakwal a ranar Talatar da ta gabata.

Rahotanni da sanadin jaridar The Punch sun bayyana cewa, marigayi Ihuigwe ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar 16 ga watan Satumba na shekarar da ta gabata a garin Rumuekini dake karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar.

An cafke mutane 4 da laifin kisan wani jigo na jam'iyyar PDP a jihar Ribas

An cafke mutane 4 da laifin kisan wani jigo na jam'iyyar PDP a jihar Ribas

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan mutane sun jefa gawar shugaban jam'iyyar cikin gonar Rogo bayan sun aikata ta'addanci kan marigayi Heaven.

KARANTA KUMA: An yi kira ga Kotu ta tsige Alkalin da ya tasa Bukola Saraki a gaba

A yayin ganawa da manema labarai, mataimakin kwamishinan 'yan sanda na jihar Mista Cyril Okoro ya bayyana cewa, jami'an tsaro karkashin jagoranci babban jami'i, Benneth Igwe, su suka taka rawar gani wajen damko wannan miyagu.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa 'yan Najeriya wani sabon alkawali a yayin ziyarar aiki da ya kai jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel