Wahalan man fetur: NNPC ta shigo da man N1.774 tiriliyan - Maikanti Baru

Wahalan man fetur: NNPC ta shigo da man N1.774 tiriliyan - Maikanti Baru

Babban kamfanin man feturin tarayya, NNPC ta ce ta shigo da man fetur daga kasar waje na kimanin kudi biliyan $5.8 wanda yake daidai N1.774 trillion.

Ta ce an shiho da wannan mai ne domin kawar da halin karanci da wahalan man fetur da al’umma ke ciki.

Babban manajan NNPC, Dakta Maikanti Kachalla Baru, ya bayyana wannan ne yayinda ya bayyana gaban kwamitin lissafi na majalisar dattawan tarayya jiya Talata a Abuja.

Baru ya bayyana cewa kamfanin NNPC ta shigo da wannan mai ne domin tabbatar da cewa yan Najeriya su tsira daga cikin mawuyacin wahalan man fetur da ake ciki.

Baru ya kara da cewa kamfanin NNPC ta dau wannan mataki ne tunda manyan yan kasuwan mai sun gaza shigo da mai saboda tsadanshi.

Wahalan man fetur: NNPC ta shigo da man N1.774 tiriliyan - Maikanti Baru

Wahalan man fetur: NNPC ta shigo da man N1.774 tiriliyan - Maikanti Baru

Yayinda yake bada tabbacin cewa za’a samu isasshen mai, ya bayyana cewa wasu yan kasuwa na karkatar da mai wasu kasashen da ke makwabtaka da Najeriya ne domin ana sayar da mai kimanin N350 ga lita a wadannan kasashen.

KU KARANTA: Sanata Ben Bruise na fuskantar sabuwar barazanar kiranye

Legit.ng Hausa na bada rahoton cewa tun shekaran 2017 da aka fara wahalan man fetur, har yanzu ba’a gushe ana fuskanta wahala ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel