Ma’aikatan Jami’a za su cigaba da yajin aiki har sai Baba-ta-gani

Ma’aikatan Jami’a za su cigaba da yajin aiki har sai Baba-ta-gani

- Ma’aikatan Jami’an Tarayya sun dade su na yajin aiki a kasar

- Dalilin haka dai Malaman Makaranta ne kurum ke aiki a yanzu

- Ma’aikatan sun ce dole Gwamnatin Tarayya ta biya bukatun su

Gwamnatin Tarayya har yanzu ba ta dauki mataki na kawo karshen yajin aikin da Ma’ikatan Jami’o’i su ke yi ba. Yau dai an yi kwanaki kusan 80 kenan ana yajin aiki a Jami’o’in kasar amma Gwamnatin Shugaba Buhari tayi shiru.

Ma’aikatan Jami’a za su cigaba da yajin aiki har sai Baba-ta-gani

An rufe sashen Makarantu saboda yajin aiki

Ma’ikatan Jami’o’in Tarayyar sun yanke hukunci cigaba da yajin da su ke yi har sai Gwamnatin Kasar ta amsawa bukatu su. Shugaban kungiyoyin hadakar da su ka tafi yajin na Jami’ar Legas ya bayyanawa Sahara Reporters wannan.

KU KARANTA: An fara dogon tattaki domin nuna adawa ga Buhari

Kwamared Kehinde Ajibade yayi tir da halin da Gwamnatin ta nuna game da yajin aikin inda yayi kira ga Ministan ilmi ya karrama maganar da aka yi da Gwamnati a 2009. Ma’aikatan dai sun ce in ba haka ba, ba za su dawo aiki ba.

Tun kwanaki kananan Ma’aikata da sauran Ma’aikatun Jami’a su ka fara shiga yajin aikin makonni 2 domin su jawo hankalin Ministan kasar Adamu Adamu. Bayan nan ne su ka shiga yajin ba kakkautawa tun a Nuwamban bara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel