An kama mutane 17 da ke da hannu cikin kisan 'yan sanda a Gboko

An kama mutane 17 da ke da hannu cikin kisan 'yan sanda a Gboko

- Hukumar 'Yansanda ta kama mutane 17 dangane da kisan Gboko na Jihar Benue da 'yansanda a Jihar

- Guda 11 daga masu laifin su ne su ka kashe matafiya a Gboko, sauran 6 kuwa 'yansanda su ka kashe

- Mataimakin Sifeta Janar na 'Yansanda, Joshak Habila, shi ne ya bayyana hakan

Akalla mutane 17 Hukumar 'Yansanda ta kama dangane da kisan wasu matafiya a sassa daban-daban na Jihar Benue da kuma kisan jami'anta a Jihar da kuma Jihar Nasarawa da ke makotaka da ita.

An kama mutane 17 da ke da hannu cikin kisan 'yan sanda a Gboko

An kama mutane 17 da ke da hannu cikin kisan 'yan sanda a Gboko

Joshak Habila, Mataimakin Sifeta Janar na 'yansanda, wanda shi ke kula da lamarin, ya bayyana cewar an samu nasarar ma su laifin ne bisa bayanai da a ka samu daga al'umma.

KU KARANTA: Canja jadawalin zabe: Jerin Sanataci 10 da zasu sha gudumar majalisa saboda kalaman adawa

Habila ya ce 11 daga wadanda a ka kaman su na daga cikin wadanda su ka kashe matafiya 7 a ranar 31 ga watan Janairu. Sauran 6 kuwa su na daga wadanda su ka kashe 'yan sanda a Jihar. A cewar sa, tun ballewar rikicin a 31 ga watan Disamba na 2017, Hukumar ta rasa jami'ai 9.

Sai dai kuma Habila bai bayyana wadanda a ka kaman a matsayin makiyaya ko manoma ba. Ya ce ba zai fayyace hakan ba ne don sunayen su ba za ta canja a ma su laifi ba.

Ya kuma ce an samu cigaba don tabbatar da cikakken tsaro ya samu. Ya bayyana cewar shigowar Soji cikin lamarin zai taimaka sosai wurin tabbatuwar tsaro da zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel