An damke mutane 4 kan kashe-kashe a jihar Benue

An damke mutane 4 kan kashe-kashe a jihar Benue

Yayinda rikicin makiyaya da manoma ke cigaba a jihar Benue, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya tuhumci jihar Nasarawa da boye wadannan makasa.

An damke mutane 4 a jihar Nasarawa kan kisan mutane da yan sandan jihar Benue.

Shi kuma gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura, ya musanta wannan zargi cewa jiharsa bata boye masu kashe-kashe a jihar Benue.

Yan ta’addan da aka kama a garin Tunga na jihar Nasarawa tsakanin ranan 16 ga wata Fabrairu da 19 ga wata. Ana zarginsu da kisan dan sanda, Sajen Solomon Dung, wasu yan sanda da kuma al’umman jihar Benue.

An damke mutane 4 kan kashe-kashe a jihar Benue

An damke mutane 4 kan kashe-kashe a jihar Benue

Wadanda aka kama sune Alhaji Laggi; shugaban yan ta’ddan, Mumini Abdullahi, Muhammad Adamu da kuma Ibrahim Sule.

KU KARANTA: alakawan wannan jihar sun fara shirin yiwa Sanatan su kiranye

Yayin bincike sun amince da aikata wannan laifi kuma sun ambaci sunayen wadanda ke rike da makaman da suka kwace bayan sun kashe yan sanda.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel