Makiyaya sun shiga yarjejeniya da gwamnatin jihar Ekiti (hotuna)

Makiyaya sun shiga yarjejeniya da gwamnatin jihar Ekiti (hotuna)

- Gwamna Fayose na Ekiti ya shiga yarjejeniya da makiyaya a jihar

- An sanya hannu a yarjejeniyar Fayose sannan kuma sunyi rantsuwa da masu maganin gargajiya

- Ardo Mairero, sarki Fulanin jihar Kwara ne ya jagoranci taron rantsuwar

A wani taro da aka rahoto cewa an shafe tsawon sa’o’i biyu ana yinta a tsakar daren ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu da kuma safiyar ranar Talata 20 ga watan Fabrairu, makiyaya sunyi wata yarjejeniya ta hanyar rantsuwa, tare da tabbatarwa da gwamnatin jihar Ekiti da mutanen jihar wanzuwar zaman lafiya.

Makiyayan sunyi alkawarin cewa bazasu sake nuna rashin da’a, kisa ko kuma su bari dabbobinsu su afka gonakin mutane ba.

Ardo Mairero, sarki Fulanin jihar Kwara ne ya jagoranci taron rantsuwar.

Jaridar Punch ta rahoto cewa taron ya samu halartan sarkin Kano Mohammed Sanusi II, wanda ya samu wakilcin tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau.

Sauran mutanen da suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa, Muhammadu Kiruwa; shugaban hukumomin tsaro, maharba, mambobin kungiyar MACBAN, manoma, da kuma yan banga.

Makiyaya sun shiga yarjejeniya da gwamnatin jihar Ekiti (hotuna)

Makiyaya sun shiga yarjejeniya da gwamnatin jihar Ekiti (hotuna)

Makiyaya sun shiga yarjejeniya da gwamnatin jihar Ekiti (hotuna)

Makiyaya sun shiga yarjejeniya da gwamnatin jihar Ekiti

A wani al'amari na daban Legit.ng ta samu wani labari daga Transparency IT Nigeria na wani Alkali a Jihar Kano wanda yayi abin a-yaba inda yayi watsi da tayin cin hancin da aka ba sa domin ya ba canza hukuncin shari’a.

KU KARANTA KUMA: Alkali ya ki karbar cin hancin Naira Miliyan 1 da aka yi masa tayi

Babban Majistare na wani Kotu da ke Unguwar Rjiyar Zaki a Garin Kano mai suna Aminu Sulaiman Fagge ya ki karbar wannan cin hanci da aka ba shi a kan wata shari’a da ake yi. Aminu Fagge yace hakan cin zarafin shari’a ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel