Kan mage ya waye: Talakawan wannan jihar sun fara shirin yiwa Sanatan su kiranye

Kan mage ya waye: Talakawan wannan jihar sun fara shirin yiwa Sanatan su kiranye

- Sanata Ben Bruise na fuskantar sabuwar barazanar kiranye

- Dalibai da sauran gama garin mutane sun zargi Sanatan nasu da rashin alkibla

- Sanatan yana wakiltar mazabar kananan hukumomi uku ne kadai

Talakawa mazabar majalisar dattijai ta jihar Bayelsa dake a kudu maso kudancin kasar nan ta gabas sun yi barazanar fara yi wa dan majalisar su mai suna Sanata Ben Murray Bruce kiranye saboda abun da suka kira rashin ingantaccen wakilcin da yake yi musu a majalisar.

Kan mage ya waye: Talakawan wannan jihar sun fara shirin yiwa Sanatan su kiranye

Kan mage ya waye: Talakawan wannan jihar sun fara shirin yiwa Sanatan su kiranye

KU KARANTA: Kotun tarayya ta kori karar da aka shigar kan tsohon Gwamna Nnamani

Mafusatan yan mazabar da suka yi wannan ikirarin sun hada da dalibai da sauran gama garin mutane sun zargi Sanatan nasu da rashin alkibla da kuma halin ko in kula da yake nuna masu.

Legit.ng ta samu dai cewa Sanatan yana wakiltar mazabar kananan hukumomi uku ne kadai da suka hada da Nembe, Brass da kuma Ogbia.

A wani labarin kuma, Wata kungiya mai rajin tabbatar da cigaban yankin dan majalisar dattijai ta Kaduna ta tsakiya yan asalin yankin sun fara yunkurin yi wa Sanatan dake wakiltar su a majalisar dattijai watau Sanata Shehu Sani kiranye daga majalisar.

Da ya ke jawabi ga manema labarai game da yunkurin nasu, shugaban kungiyar Aliyu Sai'idu Rigachikum ya bayyana cewa sun gaji da yadda Sanatan ke sukar manufofin shugaba Buhari don haka suka yanke shawarar maido shi gida.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel