Da dumin sa: Kotun tarayya ta kori karar da aka shigar da tsohon Gwamna Nnamani kan batan Naira 5.3biliyan

Da dumin sa: Kotun tarayya ta kori karar da aka shigar da tsohon Gwamna Nnamani kan batan Naira 5.3biliyan

Wata kotun gwamnatin tarayya dake zama a garin Legas a jiya talata ta kori karar da hukumar nan dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta shigar bisa zargin da suke yi wa tsohon gwamnan jihar Enugu, Mista Chimaroke Nnamani.

Mun samu dai cewa alkalin kotun ne dai mai shari'a Chuka Obiozor ya sanar da wannan hukuncin na kotun inda kuma ya bayyana cewa sun yi hakan ne dalilin bukatar hakan da lauyoyin EFCC din suka shigar gaban kotun.

Da dumin sa: Kotun tarayya ta kori karar da aka shigar da tsohon Gwamna Nnamani kan batan Naira 5.3biliyan

Da dumin sa: Kotun tarayya ta kori karar da aka shigar da tsohon Gwamna Nnamani kan batan Naira 5.3biliyan

KU KARANTA: Wahalar mai: NNPC ta shigo da mai mai yawan gaske kawo yanzu

Legit.ng ta samu dai cewa tun farko dai a zaman kotun ta saurari lauyan hukumar ta EFCC din mai suna Mista Kelvin Uzozi inda ya bukaci kotun ta soke karar da suka shigar domin za su sake shigar da wata sabuwar karar nan gaba kadan.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a ta hannun kamfanin dake kula da albarkatun man fetur na Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) a takaice ya bayyana cewa kawo yanzu ya shigo da fetur da ya kai na $5.8 biliyan.

Hukumar ta Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban ta Dakta Mai Kanti Baru yayin da yake ansa tambayoyi a gaban kwamitin majalisar dattijai dake sa ido game da harkokin hukumar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel