Badakala: Makudan kudade Naira 1.6 biliyan sun bace a wata hukumar gwamnatin tarayya

Badakala: Makudan kudade Naira 1.6 biliyan sun bace a wata hukumar gwamnatin tarayya

Kwamitin majalisar tarayya na bangaren majalisar wakillai da ke sa ido game da harkokin ayyukan hukumomin dake kula da agajin gaggawa watau Emergency and Disaster Management a turance sun yi zargin bacewar wasu makudan kudade da suka kai Naira 1.6 biliyan.

Kwamitin dai ya tuhumi shugaban hukumar nan da ke aikin bayar da agajin gaggawa ta gwamnatin tarayya watau National Emergency Management Agency (NEMA), mai suna Alhaji Mustapha Maihaja akan bacewar kudin.

Badakala: Makudan kudade Naira 1.6 biliyan sun bace a wata hukumar gwamnatin tarayya

Badakala: Makudan kudade Naira 1.6 biliyan sun bace a wata hukumar gwamnatin tarayya

KU KARANTA: Jam'iyyar APC na yaudarar mutane game da sake fasalin kasa

Legit.ng dai ta samu cewa kwamitin majalisar ya nemi wannan karin bayani ne daga shugaban yayin da yaje kare kasafin kudin hukumar na shekarar nan ta 2018 da yanzu haka ake aiki kansa.

A wani labarin kuma, Hukumar tsaron nan ta farin kaya mallakin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, watau Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) a takaice ta ware Naira 5 biliyan a kasafin kudin shekarar nan domin sayen makaman nukiliya da sauran manyan makaman zamani.

Kamar dai yadda muke samu daga majiyar mu, hukumar rundunar tsaron ta ware akalla Naira 254.2 miliyan domin sayen makaman nukiya din sai kuma Naira 196.6 miliyan domin sayen manyan motocin alfarma biyu kirar BMW 900 RT.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel