Ba mu mu ka ruguza wani gini na APC a Kaduna ba – Inji Rudunar Sojojin Najeriya

Ba mu mu ka ruguza wani gini na APC a Kaduna ba – Inji Rudunar Sojojin Najeriya

- Sojojin Najeriya sun ce ban da su aka ruguje wani gini a Kaduna

- Mai magana da yawun Rundunar yace babu ruwan su da siyasa

- Kwanan nan Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan wani Sanatan Jihar

Mun samu labari cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun ce ko kadan babu hannun su a batun ruguza wani ofishin Jam’iyyar APC a cikin Garin Kaduna da aka yi a farkon makon nan don ba aikin su bane.

Ba mu mu ka ruguza wani gini na APC a Kaduna ba – Inji Rudunar Sojojin Najeriya

Rudunar Sojojin Najeriya sun ce ban da su a rushe gidan Hunkuyi

Mai magana da bakin Rundunar Sojin kasar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka yace Sojojin Najeriya ba su shiga cikin wannan aiki da aka yi na dagargaza gidan wani Sanatan Kasar a Unguwar Rimi da ke cikin Garin Kaduna ba.

KU KARANTA: Rusa ginin mu ba zai canza komai ba inji Shehu Sani

Janar Sani Usman yace ko Soja guda bai shiga cikin wannan aiki ba kuma abin da ake yadawa na wannan jita-jita sam ba gaskiya bane. Sani Usman yace Sojojin kasar su na nan su na cigaba da ladabi kamar yadda aiki ya tanada.

Rundunar Sojan kasar tace wasu ne ke kokarin batawa Bataliyar ta da ke Garin Kaduna suna a kuma nemi a dauke masu hankali daga aikin gaban su. Sojojin kasar dai sun ce babu abin da ya hada su da rikicin ‘yan siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel