Gidan Hunkuyi ya sabawa doka da ka'idar Jihar Kaduna inji Hukuma

Gidan Hunkuyi ya sabawa doka da ka'idar Jihar Kaduna inji Hukuma

- Kwanan nan aka dagargaza wani ofishin APC a Garin Kaduna

- Hukuma tace akwai dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki

- Rikicin cikin Jam'iyyar APC a Jihar Kaduna yayi kamari kwarai

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana dalilin da ya sa ta rusa ofishin wani bagaren APC a Unguwar Rimi da ke cikin garin Kaduna ta bakin Shugaban Hukumar KAGIS na Jihar Ibrahim Hussein.

Gidan Hunkuyi ya sabawa doka da ka'idar Jihar Kaduna inji Hukuma

Gwamnatin Kaduna tayi rugu-rugu da ofishin APC

Hukumar KASUPDA mai kula da tsare-tsaren gine-gine a Jihar Katsina ta bayyana cewa yanzu haka tana kokarin kawo gyara a Jihar inda ta ke rushe gidajen da ba su kan tsari da ka'ida. A dalilin haka ne aka rusa gidan Sanata Hunkuyi.

KU KARANTA: El-Rufai ya sa an rusa gidan Sanata Hunkuyi

KASUPDA ta bayyana cewa a farkon makon nan ta rusa wani gida a layin Sambo saboda sabawa dokar Jihar da kuma rashin biyan kudin haraji ga Jihar. Hukumar tace makwabta wannan gida sun koka da yadda tsageru su ka addabe su.

'Yar uwar Hukumar ta KASUPDA watau KADGIS ta gargadi masu wannan gida su tashi tun tuni kamar yadda mu ka samu labari. Hukumar tace dole masu filaye da gidaje a Jihar su bi dokar da aka tanada na biyan kudin haraji da bin ka'ida.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel