2019: 'Yan majalisar dattawa 10 da basu amince da sauya jadawalin zabe ba

2019: 'Yan majalisar dattawa 10 da basu amince da sauya jadawalin zabe ba

A ranar Talatar da ta gabata ne, rikicin da rabuwar kawuna a majalisar dattawa da ci gaba da faskara.

Wannan lamari ya faru ne yayin da dan majalisar mai wakiltar jihar Delta ta Tsakiya, Sanata Ovie Omo-Agege, ya tuhumi majalisar da kulla wata manufa akan shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da sauya jadawalin gudanar da zaben 2019 da majalisar ta yi.

Farfajiyar Majalisar Dattawa

Farfajiyar Majalisar Dattawa

Omo-Agege yana daya daga cikin fusatattun dattawan goma na jam'iyyar APC da suka ta fice daga majlisar a ranar laraba ta makon da ya gabata a yayin da majalisar da bayar da lamuni na sauya jadawalin zaben.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, shugaban majalisar dattawan Abubakar Bukola Saraki, ya yi watsi da dattawan goma a yayin da suke yunkurin kalubalantar tsarin na zabe, inda ciki fushi suka nufaci 'yan jaridar domin bayyana musu ra'ayoyin su.

Legit.ng ta kawo muku jerin sunanyen fusatattun dattawan 10 da mazabun su kamar haka:

1. Abdullahi Adamu (Jihar Nasarawa ta Yamma)

2. Abu Ibrahim (Katsina ta Arewa)

3. Abdullahi Gumel (Jigawa ta Arewa)

4. Ali Wakili (Bauchi ta Kudu)

5. Binta Masi Garba ( Arewacin Adamawa)

KARANTA KUMA: Zan tabbatar da managarcin mulki a kowane mataki - Buhari

6. Ovie Omo-Agege (Jihar Delta ta Tsakiya)

7. Umar Kurfi (Jihar Katsina ta Tsakiya)

8. Andrewa Uchendu (Jihar Ribas ta Gabas)

9. Benjamin Uwajumogu (Jihar Imo ta Arewa)

10. Abdullahi Yahaya (Jihar Kebbi ta Arewa)

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wata cibiya mai zaman kanta tayi kira ga kotu akan ta tsige Danladi Umar, babban alkalin da ta tasa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel