Yaki da rashawa: Wani hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan ya shafa masa kashin kaza

Yaki da rashawa: Wani hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan ya shafa masa kashin kaza

Tsohon hadimi, kuma mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Waripamo Dudafa ya na neman jangalo ma tsohon Maigidan nasa tsiya a gaban Kotu.

Jaridar Sahara ta ruwaito Dudafa ya bayyana ma wata babbar Kotu dake zamanta a jihar Legas cewa duk wasu kudaden kasashen waje da ya zuba ma uwargidar tsohon shugaba Jonatha, Dame Patience Jonathan sun fito ne daga hannun Maigidan nasa Goodluck Jonathan.

KU KARANTA: Ina tuna ma El-Rufai cewa akwai wani gida na a Zaria, idan yana so ya rusa – Iji Sanata Hunkuyi

Da yake fayyace ma Kotu yadda lamarin yake a zaman sauraron karar a ranar Talata 20 ga watan Feburairu, kamar yadda mai shari’a Mohammed Idris ya umarce shi, Dudafa yace shi fa dan aike ne kawai, kuma yana cika umarnin Maigidansa da Uwardakinsa ne kawai.

Yaki da rashawa: Wani hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan ya shafa masa kashin kaza

Jonathan da Uwargida

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin da Dudafa ke amsa tambayoyi daga lauyan hukumar yaki da rashawa, EFCC, Rotimi Oyedepo, akan ko ya san wasu mutane Festus Iyoha da Peter Arivim? Sai yace ya san suna tare da tsohon shugaban kas,a kuma ana aikensa ya basu makudan daloli don a canza su, amma yace sakon Jonathan yake isarwa da na matarsa.

Daga karshe ya tabbatar ma Kotun cewa ba sau daya ba, ba sau biyu ba, sau dayawa, Jonathan da Matarsa sun sha bashi umarni da ya kai ma mutane kudade, ko kuma ya antaya su a asusun ajiyar kudi na matar Jonathan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel