Boko Haram: Wata ɗalibar makarantar mata ta bada tabbacin mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da dalibai da dama

Boko Haram: Wata ɗalibar makarantar mata ta bada tabbacin mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da dalibai da dama

Guda daga cikin daliban kwalejin yan mata dake garin Dapchi da ta sha da kyar bayan da yan ta’addan Boko Haram suka kai mata hari, ta bayyana cewa yan ta’addan sun tafi da dalibai kawayenta da dama.

Premium Times ta ruwaito dalibar mai suna Aishatu Abdullahi tana cewa ba dukkanin daliban makarantar bane suka sha yayin da yan Boko Haram suka kai hari kwalejin, sai dai majiyar Legit.ng bata tabbatar da adadin daliban da ake tsammanin an sace ba.

KU KARANTA: Tsautsayi baya wuce ranarsa: Wasu ýan mata Uku sun yi asarar rayukansu sakamakon kulle kansu a cikin wata mota

Kwamishinan Yansandan jihar, Sunmonu Abdulmaliki ya tabbatar da faruwan harin ga majiyarmu, amma yace bashi da wata tabbacin an sace daliba ko guda. “Tabbas an kai ma kwalejin hari, amma har zuwa yau, malamai da iyayen yaran na gudanar da kirge.

Boko Haram: Wata ɗalibar makarantar mata ta bada tabbacin mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da dalibai da dama

Boko Haram

“Akwai kimanin dalibai 900, haryanzu wasu daga cikinsu na gona, wasu kuma sun dawo makaranta, amma na san nan bada jimawa b azan samu cikakken bayani game da halin da ake ciki.” Inji shi.

A daren Litinin ne yan Boko Haram suka far ma garin Dapachi, wanda yayi sanadyyar tserewar dalibai da ma sauran mutanen gari zuwa cikin daji don tsira da ransu. Amma majiyarmu ta samu tattaunawa da daya daga cikin yan matan da suka tsira.

“Ina cikin makaranta lokacin da suka iso, a daidai lokacin da muke shirin karin kumallo, suna ta harbe harbe, nan da nan kowa yayi ta kansa, ina kallo lokacin da naga suna tilasta ma wasu dalibai shiga motocinsu, kuma har suka tafi babu wani Soja da muka gani, har sai bayan da suka tafi ne, Sojoji suka iso bayan shugaban makarantar mu yayi waya.” Inji Aishatu.

Sai dai Aishatu ta musanta batun da ake yadawa na cewa wai yan ta’addan sun debi abinci daga makarantar, sa’annan tace a yanzu haka an basu hutun sati daya, sai dai tace bata da niyyar komawa don cigaba da karatu a kwalejin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel