Habɓaka tattalin arzikin jihar Kano: Ganduje ya nada Sarkin Kano muƙami mai muhimmanci

Habɓaka tattalin arzikin jihar Kano: Ganduje ya nada Sarkin Kano muƙami mai muhimmanci

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya nada mai martaba sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II shugaban kwamitin binciko hanyayoyin gayyato masu zuba hannyen jari zuwa jihar Kano.

Gwamnan ya yi ma Sarkin wannan nadi ne da nufin cin moriyar iliminsa, sanayyarsa da kuma kwarewarsa game da tattalin arziki don inganta tattalin arzikin jihar Kano, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Cikakken jawabin shugaban kasa Buhari a yayin ziyarar da ya kai jihar Adamawa

Ganduje ya sanar da nadin ne a yayin bikin kaddamar da kwamitin tare da rantsar da da yayan kwamitin a gidan gwamnatin jihar Kano, wanda ya samu halartar kwamishinonin gwamnatin jihar da kuma iyayen al’umma sarakunan gargajiyar Kano.

Habɓaka tattalin arzikin jihar Kano: Ganduje ya nada Sarkin Kano muƙami mai muhimmanci

Sarki da Ganduje

Daga cikin manufofin kwamitin, shi ne don samar da hanyoyin magance duk wasu kalubale da ke hana cigaban tattalin arzikin jihar Kano, samar da sanadin da zai turo yan kasashen su zuba hannun jari a jihar, har ma da yan kasuwan Najeriya, tare da samar da alaka mai kyau tsakanin gwmanatin jihar Kano da gwamnatin tarayya har ma da sauran gwamnatocin jihohi don cigaban tattalin arzikin Kano.

Gwamnan ya tabbatar da kudirinsa na ganin gwamnatinsa ta aiwatar da duk shawararin da kwamitin za ta bayar. A nasa jawabin, Sarki Muhammadu Sunusi II ya tabbatar ma gwamnan cewa kwamitinsa za ta yi aiki tukuru don ganin ta sauke nauyin dake rataye a wuyanta.

Rahotanni sun tabbatar da an zabo yayan kwamitin ne daga dukkanin bangarori da suka hada da gwamnati, yan kasuwa masu zaman kansu, da kuma masarautar jihar Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel