An umurci lauyan Nnamdi Kanu ya kawo shi kotu ko-da-tsiya-ko-da-arziki a 28 ga watan Maris

An umurci lauyan Nnamdi Kanu ya kawo shi kotu ko-da-tsiya-ko-da-arziki a 28 ga watan Maris

- An umurci lauyan Nnamdi Kanu ya kawo shi kotu ko-da-tsiya-ko-da-arziki a 28 ga watan Maris

- Kanu din dai ana tuhuma bisa cin amanar kasa da kuma tunzura tayar da tanzuma

Babbar kotun tarayya dake zaman ta a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a yau Talata ta umurci lauyan da ke kare hatsabibin nan Nnamdi Kanu game da tuhumar da gwamnatin tarayya ke yi masa da ya gabatar da shi a gabanta a ranar 28 ga wannan watan da muke ciki.

An umurci lauyan Nnamdi Kanu ya kawo shi kotu ko-da-tsiya-ko-da-arziki a 28 ga watan Maris

An umurci lauyan Nnamdi Kanu ya kawo shi kotu ko-da-tsiya-ko-da-arziki a 28 ga watan Maris

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi wa 'yan Najeriya sabon alkawari

Haka zalika kotun ta bayyana cewa dole ne lauyan ya gabatar da Kanu din da take tuhuma bisa cin amanar kasa da kuma tunzura tayar da tanzuma da bore a watannin baya.

Legit.ng dai ta samu cewa a baya kotun ta bayar da belin sa a ranar 25 ga watan Afrilu na shekarar bara yayin da wasu daga cikin manyan 'yan siyasar kudu maso gabashin kasar suka tsaya masa.

A wani labari kuma, Shugaban gamayyar yan majalisar dattijan kasar nan da suka fito daga arewacin Najeriya da kuma ke wakiltar mazabar jihar Nasarawa ta yamma mai suna Sanata Abdullahi Adamu a jiya yayi wa tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar, Cif Obasanjo wankin babban bargo.

Sanatan wanda kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa ne ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ko kusa bai da bakin magana da har zai bude yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika yana sukar salon mulkin sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel