Hukumar 'yan sanda ta kama wadanda suka yi kisan jihar Binuwai

Hukumar 'yan sanda ta kama wadanda suka yi kisan jihar Binuwai

- Kwanaki 51 kenan da kisan jihar Binuwai

- Hukumar 'yan sanda ta kama wadanda suka yi kisan a yau

- DIG Habila Joshak shine wanda ya jagoranci tawagar kamo 'yan ta'addar

Hukumar 'yan sanda ta kama wadanda suka yi kisan jihar Binuwai

Hukumar 'yan sanda ta kama wadanda suka yi kisan jihar Binuwai

Yau kwanaki 51 kenan, da wasu makiyaya suka shiga kauyukan Guma da Logo na jihar Binuwai, inda suka kashe mutane 73, da yawa daga ciki mata ne da yara, 'yan sanda sun samu nasarar kama wadanda ake zargin. Majiyar mu Legit.ng ta bayyana cewar an kama wadanda ake zargin su hudu a kauyen Tunga dake jihar Nasarawa a watan Fabrairun wannan shekarar.

DUBA WANNAN: An bayyana Shugaba Buhari a matsayin na daya a bangaren habaka tattalin arziki Najeriya

'Yan sanda sun shaidawa majiyar mu cewar, sun samu damar kama wadanda ake zargin ne, saboda kisan Sgt. Solomon Dung da kuma wasu 'yan sanda da suka yi.

Shugaban Hukumar 'Yan sanda na Najeriya, Ibrahim Idris, shi ne ya bada umarnin kama duk wani wanda yake da alaka da kisan da akayi a jihar ta Binuwai, sannan kuma ya umarci mutanen shi da su kama duk wanda aka samu da makamai ba bisa ka'ida ba.

DIG Habila Joshak, shine ya jagoranci tawagar 'yan sandan domin kamo wadanda ake zargin.

An bada sunayen wadanda ake zargin sune: Alhaji Laggi, mai shekaru 40, wanda kuma shine shugaban kungiyar ta su, sai kuma Mumini Abdullahi, mai shekaru 34; Muhammed Adamu, mai shekaru 30; da kuma Ibrahim Sule, mai shekaru 32.

"Wadanda ake zargin sun amsa laifin su, inda suka tabbatar da cewar sun aikata laifin da ake tuhumar su dashi.

DIG Habila Joshak, shine ya yi magana da manema labarai a madadin IGP Ibrahim Idris, a yau a garin Makurdi na Jihar Benue.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel