Cikakken jawabin shugaban kasa Buhari a yayin ziyarar da ya kai jihar Adamawa

Cikakken jawabin shugaban kasa Buhari a yayin ziyarar da ya kai jihar Adamawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana gwamnatinsa ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen tona asirin barayin kudaden gwamnati ba, kamar yadda jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a jawabin da yayi a ziyarar da ya kai jihar Adamawa a ranar talata 20 ga watan Feburairu, inda yay aba ma gwamnatin jihar Adamawa game da kokarin da take yin a yaki da rashawa a jihar.

KU KARANTA: Tsautsayi baya wuce ranarsa: Wasu ýan mata Uku sun yi asarar rayukansu sakamakon kulle kansu a cikin wata mota

“Idan za’a tuna a ranat 29 ga watan Mayun shekarar 2015, na bayyana cewa rashawa da matsalar tsaro sune manyan matsalolin kasar nan, a yau ina alfaharin muna magance matsalolinmu, duk da cewa a tsarin mulkin da muke gudanarwa na mulki bai bamu damar shiga sha’anin jihohi ba, ina farin cikin yadda jihar nan ke magance rashawa a matakin kananan hukumomi.

Cikakken jawabin shugaban kasa Buhari a yayin ziyarar da ya kai jihar Adamawa

Buhari a jihar Adamawa

“Hadin gwiwa, kyakkyawar alaka tsakanin bangaren zartarwa da na dokoki tare da bin doka da ka’ida musamman ta bangaren tara kudaden shiga da kashesu sun taimaka mana sosai wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan. Ina kira ga sauran jihohi da su yi koyi da Adamawa.” Inji Buhari

Buhari ya karkare jawabinsa da cewa “Irin ayyukan da na tarar a jihar Adamawa, musamman ma a Yola, sun bani kwarin gwiwa game da cigaban jihar nan , ina fata za’a cigaba da wannan kokarin. Ina jinjina ma gwamnatin jihar Adamawa, ku cigaba da aiki.”

Daga karshe shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba ma al’ummar jihar bisa gudunmuwa da goyon baya da suke baiwa gwamnan jihar, Bindow Jibrilla, sa’annan ya bukaci da su cigaba da taimakon gwamnatin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel