Majalisar Dattawa za ta binciki wata badakala a kamfanin NNPC

Majalisar Dattawa za ta binciki wata badakala a kamfanin NNPC

- Majalisa na zargin kamfanin NNPC da shiga wata sabuwar badakala

- Dino Melaye yace kamfanin mai ya bude wani akawun dabam a boye

- Za a binciki asusun kamfanin kasar nan tsaf da makonni masu zuwa

Mun samu labari cewa Majalisar Dattawa za ta binciki wata badakala a kamfanin man Najeriya na NNPC. Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kan ta tace dole a kawo gyara dama a harkar.

Majalisar Dattawa za ta binciki wata badakala a kamfanin NNPC

Sanata Dino Melaye yace ya dace a duba asusun kamfanin NNPC

Majalisar Kasar nan za tayi bincike game da wasu kudi da ake zargi su na yawo a kamfanin mai na NNPC a asirce wanda sun haura Naira Biliyan 32. Sanata Dino Melaye ya kawo wannan kudirin a Majalisa inda aka yi na’am da shi.

KU KARANTA: PDP ta fallasa wasu kudi da aka wawure a Gwamnatin Buhari

Sanata Sam Anyawu yayi caraf ya amince da yunkurin Sanatan na Jihar Kogi wanda ya kawo maganar cewa ya kamata a binciki asusun Kamfanin NNPC da kamfanin mai na Agip inda aka bada makonni 4 a gama wannan bincike.

A zaman makon nan ne Majalisar ta kawo wannan magana inda tace akwai alamun cewa NNPC ta bude wani sabon akawun a boye wanda ba a san da zaman shi ba saboda bai da lambar BVN na tantance kowane asusun Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel