An yi kira ga Kotu ta tsige Alkalin da ya tasa Bukola Saraki a gaba

An yi kira ga Kotu ta tsige Alkalin da ya tasa Bukola Saraki a gaba

Wata cibiya mai zaman kanta dake garin Abuja, Kingdom Human Rights Foundation International, ta nemi kotu ta tsige Alkalin da ya tasa Bukola Saraki a gaba, Danladi Umar, a sakamakon zargin rashawa da hukumar EFCC take yi akan sa.

Da sanadin lauyan ta, Mista Okere Nnamdi, cibiyar ta shigar da korafin ne a ranar Juma'ar da ta gabata kamra yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Bukola Saraki da Danladi Umar

Bukola Saraki da Danladi Umar

Korafin ya nemi umarni na shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma majalisar dokoki ta kasa, akan su yi amfani da karfi ikon su kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar wajen tsige Alkalin.

KARANTA KUMA: Wani ɗan sandan bogi ya shiga hannu yayin karbar rashawar N15, 000 a garin Abuja

Tun a ranar 2 ga watan Fabrairu ne, hukumar ta EFCC da sanadin wani lauya, Mista Festus Keyamo, ta shigar da korafin har gaban babbar kotun kasar nan, inda take tuhumar Danladi Umar da laifukan cin hanci da rashawa.

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar ta hana yiwa tattalin arziki zagon kasa tana zargin Danladi da neman cin hanci har na N10m na wata shari'a da yake gudanarwa akan Rasheed Owolabi Taiwo yun a shekarar 2012.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kasafin kudi na 2018 ya tanadar da N221m ga wasu ma'aikatu biyar da za su batar wajen kayatar da su a fannin ci da sha.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel