Kiri da muzu: Gwamna El-Rufai ya nesanta kansa da batun rushe gidan Sanata Hunkuyi

Kiri da muzu: Gwamna El-Rufai ya nesanta kansa da batun rushe gidan Sanata Hunkuyi

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya barranta kansa da batun da ake yadawa game da cewa wai yana da hannu cikin aikin rushe gidan Sanata Suleiman Othman Hunkuyi a garin Kaduna.

Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda ya daura wata sanarwar daga hukumar tsara biranan jihar Kaduna, KASUPDA, wanda take bayyana cewar ita ce ta rushe gidan Sanatan.

KU KARANTA: Wani direban bankaura ya kira ruwa, ya shiga gaban motar gwamna, ya hana shi tafiya

A cikin sanarwar, KASUPDA ta bayyana cewa ta a yanzu haka tana gudanar da aikin shawo kan ayyukan barace barace, kawar da duk wasu gine gine da aka gina su ba a kan ka’ida ba, da kuma dawo da fasalin jihar Kaduna.

Kiri da muzu: Gwamna El-Rufai ya nesanta kansa da batun rushe gidan Sanata Hunkuyi

Gidan Sanata Hunkuyi

Legit.ng ta ruwaito KASUPDA tana cewa “Da safiyar ranar Talata 20 ga watan Feburairu, mun kawar da wani gini dake lamba 11B kan titin Sambo saboda karya dokar amfani da fili, tare da rashin biyan harajin kudin kasa tun daga shekarar 2010.

“Mun kai takardar kashedin rusa gidan zuwa gida mai lamba 28 titin Inuwa Wada, inda kamfanin da ta mallaki gidan titin Sambo ke zaune, yanzu dai filin ya koma hannun KASUPDA don gina wajen shakatawa ga jama’a mazauna unguwar.” Inji KASUPDA

Daga karshe KASUPDA na sanar da jama’a da suka mallaki gida ko kadara da su hanzarta zuwa biyan harajinsu, haka zalika ta gargadi jama’a da su guji canza amfanin da suka mallaki fili saboda shi ba tare da bin ka’ida ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel