Rundunar Sojojin Najeriya sun shirya yaki da Makiyayan da su ka addabi Jama’a

Rundunar Sojojin Najeriya sun shirya yaki da Makiyayan da su ka addabi Jama’a

- Rundunar Sojojin Najeriya za su magance rikicin Makiyaya

- Shugaban Hafsun Soji ya gana da Gwamna Ortom na Benuwe

- Sarkin Garin Ayatse ya ji dadin zuwan Rundunar Sojojin kasar

Yanzu mu ka samu labari cewa Rundunar Sojin Najeriya ta fara shirye-shiyen kawo karshen rikicin Makiyaya da Manoma a kasar nan da ya fitini Jama’a a fadin kasar musamman Yankin Benuwe.

Rundunar Sojojin Najeriya sun shirya yaki da Makiyayan da su ka addabi Jama’a

Buratai ya gana da Mai Girma Gwamnan Benuwe. Hoto daga: Benue Press

Rundunar Sojojin Kasar nan za ta fara wani sabon sintiri da ‘Operation Cat Race Exercise’ a Jihar Benuwe domin magance rikicin Makiyaya da ya addabi mutanen garin. Sarkin Kasar Tibi James Ayatse ya yabawa kokarin Rundunar.

KU KARANTA: Sojoji sun kusa cafke Shugaban Boko Haram Shekau

Rundunar Sojojin Najeriya sun shirya yaki da Makiyayan da su ka addabi Jama’a

Rundunar Sojojin za su kafa ‘Operation Cat Race Exercise’

Yanzu haka Shugaban Hafsun Sojin kasar Laftana Janar Tukur Buratai yana Garin Makurdi inda ya ziyarci Gwamna Samuel Ortom a gidan Gwamnatin Jihar. Gwamna Ortom ya tarbi Janar Buratai ne sanye da kayan Sojojin sa.

A farkon makon nan mun ji cewa Janar Tukur Buratai ya ziyarci fadar Sarkin Kasar Tibi. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Hafsun Sojojin kasar ya dawo bakin aiki bayan rasuwar Mahaifin sa kwanakin baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel