Sanata Hunkuyi ya maida martani ga El-Rufai

Sanata Hunkuyi ya maida martani ga El-Rufai

- Sanata Suleiman Hunkuyi ya maida wa Gwamna Nasir El-Rufai martani

- A yau ne gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya saka aka rushe gidan Sanata Hunkuyi dake garin Kaduna

Sanata Hunkuyi ya maida martani ga El-Rufai

Sanata Hunkuyi ya maida martani ga El-Rufai

A safiyar yau ne gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin gwamna Nasir El-Rufai ta aika da ma'aikata suka rushe gidan Sanata Suleiman Hunkuyi, dake kan Sambo Road, a cikin garin Kaduna.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Tarayya zata bayyana wadanda zasu saka hannun jari a sabbin matatun man fetur da ake ginawa - Kachikwu

Hakan ta taba faruwa akan Shugaban Jam'iyyar APC mai wakiltan arewa maso yamma, Alhaji Inuwa Abdulkadir, watannin da suka gabata. Inda shima aka tura ma'aikata suka rushe gidan shi a cikin birnin Kadunan.

Kwanakin baya gwamnan ya taba tura masu rushe gidan akan suje su rushe gidan, sai dai basu samu dama ba, inda matasan unguwar suka hana rushe gidan. Dalilin da ya saka su hakura da rushe gidan.

Sanatan ya maida wa gwamna El-Rufai martani, inda yake cewa yana mulkin kama karya, sannan kuma ya kasa jure adawar siyasar sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel