Kasafin kudin 2018: Ma'aikatu 5 za su batar da N221 wajen ci da sha

Kasafin kudin 2018: Ma'aikatu 5 za su batar da N221 wajen ci da sha

Kimanin N221, 015, 898 aka kiyasta za a batar a ma'aikatu biyar wajen kayatar da su ta fuskar ci da sha a cikin kididdigar kasafin kudi na 2018.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan ma'aikatu sun hadar da ma'aikatar kudi, kasafi da tsare-tsare, masana'antu, labarai da kuma ma'aikatar noma.

Ministan Kudi; Kemi Adeosun

Ministan Kudi; Kemi Adeosun

Cikin wannan ma'aikatu biyar, ma'aikatar labarai me shiyoyi 21 zata samu kaso mafi tsoka na kimanin N113.1m, wanda ya lunka kudaden da aka ware wa ma'aikatar kudi mai shiyoyi 47 da suka tasar ma N52.7m.

KARANTA KUMA: Da a ce na sauya sheka zuwa APC, tuni da na zamto minista - Babangida Mu'azu

Legit.ng ta fahimci cewa, kudaden da aka ware domin ma'aikatar ta labarai sun lunka na ma'aikatar noma har sau 13 wadda take dauke da cibiyoyi 39, inda ta samu kimanin N10.7m.

Ma'aikatar kasafi da tsare-tsaren kasa kuma ta samu N31.5m, inda ma'aikatar masana'antu da kasuwanci ta samu kaso na N12.8m.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel