Gwamnan Kaduna ya nada wasu muhimman makamai

Gwamnan Kaduna ya nada wasu muhimman makamai

- Gwamnatin Jihar Kaduna tayi wasu sababbin nadi a farkon makon nan

- Gwamna El-Rufai ya nada mata sun shugabanci KADIPA da KADSTRA

- Kwanan nan aka kafa Hukumar KADSTRA na motocin haya a Kaduna

Mai Girma Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya nada wasu muhimman makamai a Gwamnatin sa wannan makon kamar yadda labari ya zo mana daga mai magana da yawun mai girma Gwamnan watau Mista Samuel Aruwan.

Gwamnan Kaduna ya nada wasu muhimman makamai

Gwamnan Jihar Kaduna Malam El-Rufai

Gwamna El-Rufai ya nada Shugabannin Hukumar KADIPA da na KADSTRA. Hajiya Umma Aboki ne aka saba domin ta shugabanci Hukumar KADIPA ta Jihar Kaduna. Haka kuma Aisha Saidu-Bala za ta rike babban ofishin KADSTRA.

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna ya rusa gidan wani Sanatan Jihar

Saidu-Bala tayi aiki a wurare da dama a Turai da Afrika da ma Amurka. Wannan Baiwar Allah tana cikin wadanda su ka yi aikin wata hanya ta karkashin kasa a Birnin Landan inda tayi karatun ta har na Digiri da Digirgir sa sauran su.

Umma kuwa kwararriyar ma'aikaciyar banki ce na sama da shekaru 20. Umma tana da Digiri na biyu a harkar tattali kuma da ita ce mai ba Gwamna shawara a lamuran. Ita ma dai Aisha ta na cikin masu ba Gwamnan shawara kafin a kara mata matsayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel