Masana tarihi a Amurka sun fitar da jerin shugabannin kasar 10 da suka fi kwazo a mulki

Masana tarihi a Amurka sun fitar da jerin shugabannin kasar 10 da suka fi kwazo a mulki

- Shugaban kasar Amurka na yanzu, Donald Trump, ne yafi ragowar shugabannin kasar lalacewa

- Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, bakin mutum na farko da ya shugabanci kasar, na daga cikin shugabannin kasar 10 mafi kwazo a ofis

- Farfesan kimiyyar siyasa, Brandon Rottinghaus, na jami'ar Houston da wasu masana su ka gudanar da binciken

Wani bincike da Farfesan kimiyyar siyasa, Brandon Rottinghaus, a jami'ar Houston da Justin S. Vaughn, mataimakin Farfesa a sashen kimiyyar fasaha a jami'ar jihar Idaho dake kasar Amurka sun bayyana shugaban kasar Amurka mai ci, Donald Trump, a matsayin mafi lalacewa a cikin shugabannin da suka mulki kasar.

Masana tarihi a Amurka sun fitar da jerin shugabannin kasar 10 da suka fi kwazo a mulki

Masana tarihi a Amurka sun fitar da jerin shugabannin kasar 10 da suka fi kwazo a mulki

Binciken ya kunshi jin ra'ayin masana ilimin siyasa 170 dake nazarin duk shugaban da ya mulki Amurka.

KU KARANTA: An mayar da sauraron karar 'yan Boko Haram 73 Abuja

An buga sakamakon binciken da suka gudanar a wata jaridar kasar Amurka, Times, a jiya Litinin.

Barack Obama ya tashi daga mataki na 18 da yake a rahoton binciken 2014 ya zuwa cikin jerin shugabannin kasar 10 mafi kwazo.

Binciken na wannan shekarar ya canja tsohon rahotannin baya da suka jibge shugaban kasar Amurka, Buchanan, a matsayin mafi lalacewa. Yanzu Trump ya hau matakin Buchanan.

Tsohon shugaban kasa Bill Clinton ya fado daga cikin jerin shugabannin 10 mafi kwazo ya zuwa mataki na 13, kazalika tsohon shugaba Andrew Jackson ya fado daga mataki na 9 zuwa na 15.

Masu binciken sun bayyana cewar shugaba Trump na da damar inganta kimar sa a bincike na gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel