Majalisar dattawa tayi Allah wadai da rushe sakatariyar APC da El-Rufai yayi

Majalisar dattawa tayi Allah wadai da rushe sakatariyar APC da El-Rufai yayi

Majalisar dattawa tayi Allah wadai da rushe sakatariyar sashen jam’iyyar APC a jihar Kaduna.

Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin jihar Kaduna ta rushe ofishin bangaren jam’iyyar APC da ta dakatar da gwamna Nasir El-Rufai a ranar Talata, 20 ga watan Fabarairu.

Da yake Magana a zauren majalisa a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu, dan majalisa mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya bayyana cewa El-Rufai da kansa ya yi jagoranci tare da kula da rushe ofishin sashen jam’iyyar APC din.

Majalisar dattawa tayi Allah wadai da rushe sakatariyar APC da Rl-Rufai yayi

Majalisar dattawa tayi Allah wadai da rushe sakatariyar APC da Rl-Rufai yayi

A nashi bangaren, mataim akin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu yace baza a taba cimma mulkin damokradiyya ba a karkashin irin wannan danniyan da tauye hakki ba.

KU KARANTA KUMA: Zamu marawa Buhari baya idan ya sake takara a 2019 – Dattawan kudu maso gabas

Kamar yadda muka kawo maku a baya Gwamnatin jihar Kaduna ta rusa Hedkwatar sashin jam’iyyar APC da ta dakatar da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, har na tsawon watanni shida.

Legit.ng ta samu rahoton cewa, an rusa ofishin ne dake gida mai lamba 11B, Sambo road, GRA Kaduna,da kariyan jami’an tsaro da misalin karfe 4 na safiyan ranar Talata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel