Adadin kananan yaran dake fama da yunwa a Najeriya ya Karu

Adadin kananan yaran dake fama da yunwa a Najeriya ya Karu

- UNICEF ta ce adadin kananan yaran dake fama da yunwa a Najeriya ya Karu

- Hukumar UNICEF ta ce yaran dake fama da rama saboda yunwa sun karu daga kashi 24.2% zuwa 31.5% bisa 100

Asusun samar da tallafi ga kananan yara (UNICEF) dake karkashin Majalissar Dinkin Duniya (UN) ta bayyana cewa adadin kananan yara dake fama da yunwa a Najeriya sun karu.

Jakadar hukumar hukumar UNICEF a Najeriya, Zubie-Okolo, ta bayyana haka ne a wani taro na musamman da aka gudanar akan wannan matsala a jihar Enugu.

Zubie-Okolo, ta ce al’amarin ya karu ne a Najeriya daga shekaru biyar da suka gabata.

Adadin kananan yaran dake fama da yunwa a Najeriya ya Karu

Adadin kananan yaran dake fama da yunwa a Najeriya ya Karu

Okolo ta ce binciken da hukumar ta gudanar a shekarar 2017 a gidaje 33,901 a jihohin kasar nan ya nuna cewa yaran dake fama da rama saboda yunwa ya karu daga kashi 24.2 zuwa 31.5 bisa 100.

KU KARANTA : Zubar da jini ya fi man fetur sauki a Najeriya – Shehu Sani

Sai kuma yaran da yunwa ya hana su girma sun karu suma daga kashi 34.8 zuwa 43.6 bisa 100 sannan adadin yaran da yunwa ke yin ajalin su ya karu daga kashi 10.2 zuwa 10.8.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel