An mayar da sauraron karar 'yan Boko Haram 73 Abuja

An mayar da sauraron karar 'yan Boko Haram 73 Abuja

- Za a cigaba da sauraron karar wasu mayakan kungiyar Boko Haram 73 a Abuja

- An mayar da sauraron karar Abuja ne saboda mayakan sun ki amsa laifinsu

- Gwamnatin tarayya na kokarin samar da hanya mafi sauki da zata gudanar da shari'ar mayakan kungiyar Boko Haram fiye da 6,000 dake tsare a sansanin soji

An mayar da karar mayakan kungiyar Boko Haram 73 da basu amsa laifinsu ba zuwa Abuja.

Mayakan na daga cikin 'yan kungiyar 301 da kotun tarayya dake Bussa a jihar Naija ke sauraro.

An mayar da sauraron karar 'yan Boko Haram 73 Abuja

An mayar da sauraron karar 'yan Boko Haram 73 Abuja

Bayan mayakan sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa sai kotun ta daga sauraron karar ya zuwa ranakun 24 da 25 na watan Afrilu domin bawa gwamnati damar gabatar da shaidun ta.

KU KARANTA: Dokar hana kiwo cikin dare da Gwamna Fayose ya kafa kariya ce ga makiyaya - Sarkin Kano

Wata majiya a kotun ta tabbatar da cewar kotun ta saki wasu daga cikin wadanda aka gurfanar saboda rashin gamsashshiyar hujja, tabin hankali, ko kuma karancin shekaru.

Gwamnatin tarayya na kokarin samar da hanya mafi sauki da zata gudanar da shari'ar mayakan kungiyar Boko fiye da 6,000 dake tsare a sansanin soji a Maiduguri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel