An mayar da miji na saniyar ware bayan APC ta ci zaben 2015 - Uwargidar Tinubu

An mayar da miji na saniyar ware bayan APC ta ci zaben 2015 - Uwargidar Tinubu

- Sanata Oluremi, Matar Bola Tinubu, ta ce an yakice mijin na ta bayan APC ta ci zaben 2015

- Ta bayyana hakan ne a ranar Litini yayin wani shiri na bayyana ra'ayoyi a wani gidan talabijin

- Ta ce mijin ta mutum ne da soyayyar sa ga Najeriya ya hana shi bijirewa Fadar Shugaban Kasa duk da yakice shi da a ka yi

A yayin da Asiwaju Bola Tinubu, Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa, ya fara sasantawa tsakanin 'yan jam'iyyar, matar sa, Sanata Oluremi Tinubu, ta fito ta koka da yadda a ka wofintar da mijin ta bayan APC ta ci zaben 2015.

Sanatar ta fadi hakan da ta bayyana a wani shiri na bayyan ra'ayi da safiyar ranar Litini da tashar talabijin na 'Television Continental'. Ta koka da yadda a ka jakice shi a ka mayar da shi saniyar ware duk da irin gudummuwar da ya bayar don tabbatar da jam'iyyar ta ci zaben.

Misis Tinubu ta bayyana cewar kokarinta na neman mijin na ta ya bijirewa Fadar Shugaban Kasa ya ci tura, don kuwa kishin Kasa kawai ke gaban shi. A cewar ta, gaskiya tsakanin ta da Allah ta fada, mijin ta mutum ne da ke cike da soyayyar kasar nan.

Ta kuma ce duk da yadda Gwamnatin Buhari ke fuskantar Soke da korafe-korafe, har yanzun Buhari ne dan siyasar da ya cancanta, shi ne zai lashe zaben 2019 mai zuwa.

Ta ce ba wai ta na ma sa kamfe ba ne, amma gaskiyan lamari shi ne, idan a ka lura har yanzun talakawa sun yarda da Buhari. Idan a na maganar gaskiya da rikon amana ne, to Buhari za a nuna. ''Ban dai san a yanzun ba''. In ji ta.

An mayar da miji na saniyar ware bayan APC ta ci zaben 2015 - Uwargidan Tinubu

An mayar da miji na saniyar ware bayan APC ta ci zaben 2015 - Uwargidan Tinubu

KU KARANTA: Dokar hana kiwo cikin dare da Gwamna Fayose ya kafa kariya ce ga makiyaya - Sarkin Kano

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel