Gwamnatin Tarayya zata bayyana wadanda zasu saka hannun jari a sabbin matatun man fetur da ake ginawa - Kachikwu

Gwamnatin Tarayya zata bayyana wadanda zasu saka hannun jari a sabbin matatun man fetur da ake ginawa - Kachikwu

- Za a bayyana wadanda zasu saka hannun jari a sabbin matatun mai da ake ginawa

- Ibe Kachkwu shi yayi wannan sanarwar a wurin wani taro

- Ya ce nan ba da dadewa ba Najeriya zata zama daya daga cikin manyan kasashe da suke da wadatar mai

Gwamnatin Tarayya zata bayyana wadanda zasu saka hannun jari a sabbin matatun man fetur da ake ginawa - Kachikwu

Gwamnatin Tarayya zata bayyana wadanda zasu saka hannun jari a sabbin matatun man fetur da ake ginawa - Kachikwu
Source: Depositphotos

Karamin Ministan Man Fetur, Mista Ibe Kachikwu, ya sanar da cewar a watan Maris din nan gwamnatin tarayya za ta bayyana sunayen wadanda zasu saka hannun jari a sababbin matatun mai da ake ginawa a kasar nan. Da yake jawabi a wani taro da aka gudanar na man fetur, Kachikwu ya ce gwamnati zata bi duk wata hanya domin ganin ta tilasta wa kamfanonin man fetur dana gas da ke aiki a kasar nan wurin ganin sun gina matatun mai a kasar.

DUBA WANNAN: Kokarin da Buhari yayi akan Boko Haram shine yasa ni barin jam'iyyar PDP - Ahmad Gulak

Ministan ya ce, lokaci na nan zuwa da gwamnati ba za ta sake yarda da kamfanonin man fetur na kasar nan su dinga fita da danyen mai ba, domin zuwa wata kasa tacewa.

A halin yanzu babu wani kamfanin man fetur a Najeriya da yake tace mai da kanshi, amma dai akwai alkawarin da kungiyar kamfanonin man fetur ta duniya wato (IOC) a takaice ta yi kwanan nan, na cewar za a gina wurin tace man, ko kuma a gyara daya daga cikin wadanda muke da su a kasar nan.

"Zamu kai wani mataki da kasar Najeriya zata zama daya daga cikin kasashen da suke tace man fetur a duniya." Inji Kachikwu.

Da yake jawabi, ministan ya ce, kamata yayi man fetur ya zama daya daga cikin muhimman abubuwan da suke ciyar da kasar nan gaba, kuma ya zamo daya daga cikin abubuwan da suke samar da aiki ga al'umma. Sannan ya zamo abinda zai fito da kimar kasar nan a idon sauran kasashen duniya.

"Manufa da nake da ita shine, nan da shekaru 10 masu zuwa, Najeriya ta kasance ta wadata da man fetur. Cibiyoyin Najeriya da masu hannun jari za su fara tashi daga kashi 10 cikin dari zuwa kashi 40 ko 50 cikin dari na hannun jari."

Ministan ya ce tun lokacin da aka fara gasar 7Big shekaru biyu da suka wuce, gwamnati ta samu damar canza tsarin kudin da ake amfani da su wajen bunkasa masana'antu.

"Yanzu mun fara ganin ayyukan kamar Egina, $15bn; Zabazaba, $10bn; Bonga, $10bn, da kuma sauran kamfanoni masu yawa sun sanya fiye da $40bn na hannun jari a cikin shekaru biyar masu zuwa, idan muka cigaba da yanda muke, "in ji shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel