Da a ce na sauya sheka zuwa APC, tuni da na zamto minista - Babangida Mu'azu

Da a ce na sauya sheka zuwa APC, tuni da na zamto minista - Babangida Mu'azu

Tsohon gwamnan jihar Neja, Dakta Babangida Mu'azu Aliyu na jam'iyyar adawa ta PDP, ya bayyana cewa tuni da yanzu ya kasance minista da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Babangida ya bayyana haka ne a ranar Litinin din da ta gabata a birnin Minna, yayin sauyin sheka na wasu 'yan siyasa 34, 826 zuwa jam'iyyu daban-daban da suka hadar har da mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Aminu Yusuf.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, da yawan 'yan siyasar da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC makusanta tsohon gwamnan jihar ne.

Dakta Babangida Mu'azu Aliyu

Dakta Babangida Mu'azu Aliyu

Tsohon gwamnan yake cewa, ba ya da ra'ayin sauya sheka zuwa APC a sakamakon aminci da kuma imani da yake da shi na jam'iyyar PDP.

KARANTA KUMA: Kasashe mafi arhar rayuwa a nahiyyar Afirka

Legit.ng da sanadin jaridar The Punch ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan ya samu damar sauya sheka zuwa APC a yayin da ya jagoranci kungiyar gwamnoni ta G-7, amma ba aikata hakan ba saboda yakinin sa ga jam'iyyar ta PDP.

Babangida ya kara da cewa, jam'iyyar PDP ce ta taka rawar gani wajen nasarar sa har zuwa kujerar gwamna.

Jaridar Legit.ng ta kuma jeranta 'yan majalisa da ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari, dake hankoron kujerun gwamnoni a jihohin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel