Harka ta baci: Dala ta shakare wuyan Naira a kasuwannin bayan fage

Harka ta baci: Dala ta shakare wuyan Naira a kasuwannin bayan fage

- Dala ta shakare wuyan Naira a kasuwannin bayan fage

- Ana saida dala 1 akan N367 a yanzu maimakon N368 din da aka saida ta a baya

- Wannan dai na zuwa ne duk da irin kudaden da babban bankin na Najeriya yake malalawa a kasuwannin

Labaran da ke zuwa mana ba da dadewa ba daga majiyoyin mu na nuni da cewa takardar kudin Naira na Najeriya ta kara ja baya idan a ka kwatanta ta da takardar kudin kasar Amurka na Dala a kasuwannin bayan fage.

Harka ta baci: Dala ta shakare wuyan Naira a kasuwannin bayan fage

Harka ta baci: Dala ta shakare wuyan Naira a kasuwannin bayan fage

KU KARANTA: Gwamnan Benue ya kammala shirin komawa PDP

Mun dai samu cewa Naira din ta kara rage daraja da maki daya a kasuwannin bayan fagen inda aka saida dala 1 akan N367 a yanzu maimakon N368 din da aka saida ta ranar kafin wannan.

Legit.ng haka zalika ta samu cewa an sayi kudin tarayyan turai da na Ingila akan N432 da kuma N478 duk dai akasuwannin canjin.

Wannan dai na zuwa ne duk da irin kudaden da babban bankin na Najeriya yake malalawa a kasuwannin domin ganin farashin ya dai-daita.

A wani labarin kuma, mun samu cewa Akalla jahohi sha daya daga cikin ashirin da ukku ne da a baya gwamnatin tarayya ta ba lamunin karbar tallafin bashi domin inganta kasafin kudin su sun anshi zunzurutun kudaden da suka kai Naira biliyan 16.1 zuwa watan Janairun shekarar nan da ya gabata.

Wannan dai na kun she ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa mataimakin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai watau Laolu Akande ya fitar dauke da sa hannun sa ya kuma rabawa manema labarai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel