Albashi na bai wuce mun kwana 7 yake karewa - Gudaji Kazaure

Albashi na bai wuce mun kwana 7 yake karewa - Gudaji Kazaure

- Albashi na bai wuce mun kwana 7 yake karewa - Gudaji Kazaure

- Dan majalisar yana wakiltar mazabar kananan hukumomin Kazaure, Roni, Yankwashi da kuma Gwuiwa

- Ya kara da cewa sauran sati 3 na duk watan duniya da kyar da rufa-rufa yake ida su

Sanannan dan majalisar nan na tarayya a zauren majalisar wakillai mai wakiltar mazabar kananan hukumomin Kazaure, Roni, Yankwashi da kuma Gwuiwa dake a jihar Jigawa ya bayyana wa duniya cewa shi fa albashin sa kwana 7 yake yi masa shikenan ya rabar da shi ga al'umma.

Albashi na bai wuce mun kwana 7 yake karewa - Gudaji Kazaure

Albashi na bai wuce mun kwana 7 yake karewa - Gudaji Kazaure

KU KARANTA: Boko Haram: Shin akwai ma su yi wa Buhari zagon kasa kuwa?

Mun samu dai cewa dan majalisar yayi wannan ikirarin ne lokacin da yake zantawa da jama'ar mazabar sa da suka je masa ziyarar jadaddagoyon baya inda ya bayyana cewa shi kudin sa ba na ajiye wa bane da ya samu yake bayar wa.

Legit.ng ta samu dai daga majiyar ta mu cewa dan majalisar ya kara da cewa sauran sati 3 ko kuma kwanaki 21 zuwa 23 na duk watan duniya da kyar da rufa-rufa yake ida su don kuwa dukkan abun da ya mallaka ya riga da ya rabarwa jama'ar sa.

A wani labarin kuma, mun samu cewa Shugaban gamayyar yan majalisar dattijan kasar nan da suka fito daga arewacin Najeriya da kuma ke wakiltar mazabar jihar Nasarawa ta yamma mai suna Sanata Abdullahi Adamu a jiya yayi wa tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar, Cif Obasanjo wankin babban bargo.

Sanatan wanda kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa ne ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ko kusa bai da bakin magana da har zai bude yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika yana sukar salon mulkin sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel