Dalilina na bawa Buhari shawarar ya dakatar da gurfanar Bello Adoke a kan badakalar Malabu - Ministan shari'a

Dalilina na bawa Buhari shawarar ya dakatar da gurfanar Bello Adoke a kan badakalar Malabu - Ministan shari'a

- Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya kare kansa a kan takardar shawarar dakatar da gurfanar da tsohon ministan shari'a, Bello Adoke, a kan badakalar Malabu da ya aikewa Buhari

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da tsohon ministan man fetur, Dan Etete, da wasu manyan jami'an gwamnatin Jonathan a kan badakalar kudin Malabu, $1.1bn

- Malami ya ce ya shawarci Buhari ya dakatar da gurfanar da Bello Adoke bayan nazarin hujjojin da gwamnati dake da su a kansa, wadanda ya ce basu da karfi

Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya kare kansa dangane da takardar shawarar dakatar da gurfanar da tsohon ministan shari'a, Bello Adoke, a kan badakalar kudi, dala biliyan $1.1, na Malabu da ya aikewa shugaba Buhari.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta shirya jerin wasu caji guda uku da suka hada da zamaba, almundahana, da safarar kudi, a kan Adoke, tsohon ministan man fetur, Dan Etete, da wasu mutane.

Dalilina na bawa Buhari shawarar ya dakatar da gurfanar Bello Adoke a kan badakalar Malabu - Ministan shari'a

Ministan shari'a, Abubakar Malami

Da yake amsa tambayar wakilin jaridar todayng a jiya Litinin, Malami, ya ce ya shawarci Buhari ne bayan nazarin cajin da gwamnatin tarayya ke da su a kan Adoke, wadanda ya ce basu da karfin da zasu saka kotu yi masa wani hukunci.

DUBA WANNAN: Labari da duminsa: Shugaba Buhari ya ja kunnen magu, ya bashi wa'adin kwana hudu ya kare kansa

A ranar Lahadi an tambayi Malami dalilinsa na shawartar Buhari a kan dakatar da karar Adoke sabanin ya yi abinda ya dace na dakatar da karar a matsayinsa na ministan shari'a, sai ya kada baki ya ce "ba wai dakatar da karar ne dalilin rubuta wasikar ta wa ba, wasikar ta fi mayar da hankali ne a kan yadda Najeriya zata ci moriyar rijiyar man fetur ta 245 wacce saboda shari'ar da ake yi an barta a wulakance".

Malami ya ce binciken EFCC ya dakatar da masu saka hannun jari daga kasashen ketare daga neman lasisin hakar man fetur daga rijiyar.

Malami ya kara da cewar wasikar ta fi mayar da hankali a kan damar da Najeriya ke da ita ta bunkasa tattalin arzikinta ta hanyar yin abinda ya dace da rijiyar man ta 245 da ake ta gwabza shari'a a kanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel