Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai hari kunar bakin wake jami'ar Maiduguri

Yanzu-yanzu: Boko Haram sun kai hari kunar bakin wake jami'ar Maiduguri

Bayan yan kungiyar Boko Haram sun sake malaman jami’ar Maiduguri guda biyu kwanakin nan, yan ta’addan sun kuma kai mumunan hari jami’ar da daren nan.

Rahotannin sun nuna cewa wani dan kunar bakin wake ya kai hari misalin karfe 7:50 na daren nan kusa da gidan kwanan dalibai.

Majiya ta bayyana cewa dan kunar bakin waken, yaro dan shekara 13 kacal ne ya rasa ransa a wannan hari.

KU KARANTA: Hukumar NHIS za ta maida hankali ne wajen yi wa jama’a aiki – Yusuf Usman

Zaku tuna cewa yan Boko Haram sun saki malaman jami’ar da sukayi garkuwa da su tun watan Yulin da ya gabata yayinda suka je hakan man fetur.

Yan ta’addan sun far ma masu hakan man inda akalla mutane 69 suka hallaka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel