Labari mai dadi: Farashin danyen man fetur ya yi tashin gwauron zabi cikin sati biyu

Labari mai dadi: Farashin danyen man fetur ya yi tashin gwauron zabi cikin sati biyu

- Ciki sati biyu kacal, farashin danyen man fetur ya yi tashin gwauron zabi

- An alakanta tashin farashin man da rigingimun dake faruwa a yankin gabas ta tsakiya da suka jawo janyewar kasashe daga cinikayya da kasashen yankin

- Farashin gangar mai a duniya na kara samun tagomashi a kasuwar duniya tun shigowar shekarar nan

Farashin danyen man fetur ya yi tashin gwauron zabi cikin sati biyu kacal da samun rahotannin karuwar darajar sa.

Darajar danyen man ta karu ne bayan wasu kasashen yankin Asiya sun yanke shawarar bin sahun kasar Amurka na janye cinikayya da kasashen yankin gabas ta tsakiya mai fama da rigingimu.

Labari mai dadi: Farashin danyen man fetur ya yi tashin gwauron zabi cikin sati biyu

Farashin danyen man fetur ya yi tashin gwauron zabi cikin sati biyu

A jiya firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewar kasar sa zata yanke huldar cinikayya da kasar Iran bayan da rikici tsakanin kasar da makobciyar ta ke kara tsamari.

DUBA WANNAN: Labari da duminsa: Shugaba Buhari ya ja kunnen magu, ya bashi wa'adin kwana hudu ya kare kansa

Karuwar farashin gangar man fetur, ga kasashen da tattalin arzikinsu ya dogara a kan fetur irin su Najeriya, abu ne mai dadi.

Saidai har yanzu a gida Najeriya jama'a na cigaba da kokawa bisa wahalar da suke sha saboda karanci da kuma tsadar man fetur.

Matsalar wahalar man fetur ba bakuwa bace a Najeriya, sai dai jama'a na ganin a wannan karon matsalar ta yi tsawon da aka dade ba a ga irinsa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel