Ya kamata mu samu wuri mu huta don lokacin matasa yayi – Soyinka

Ya kamata mu samu wuri mu huta don lokacin matasa yayi – Soyinka

- Farfesa Wole Soyinka yace a ji tsoron irin su IBB da Obasanjo

- Tsofaffin Shugabannin sun nemi Buhari ya hakura da mulki

- Sai dai Farfesan yana ganin akwai wani abu da ke ran su IBB

Tsohon fitaccen marabucin Duniya Farfesa Wole Soyinka, yayi kaca-kaca da sabuwar Kungiyar hadakar da ke kokarin koyawa Jam’iyar PDP da APC darasi da tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya kafa inda yace ba shi ba ta.

Ya kamata mu samu wuri mu huta don lokacin matasa yayi – Soyinka

Farfesa Wole Soyinka yace ya rage matasa su gyara kasar

Dattijon kasar Farfesa Wole Soyinka yace sabuwar kungiyar da Obasanjo ya bude ba ta irin su ba ce. Farfesan yace da zarar an ga irin su a cikin wannan Kungiyar ya kamata a ruga da shi wajen Likitan kwakwalwa domin a auna lafiyar sa.

KU KARANTA: Wani Matashi yayi wani nazari da zai agazawa masu cutar idanu

Farfesa Soyinka ya kuma ce dole jama’a su yi kaffa-kaffa da irin su Obasanjo da IBB inda yace ba abin da ake tunani ke cikin ran tsofaffin Shugaban kasar ba. Wole Soyinka yayi wannan bayani ne lokacin da ya tattauna da sashen yarbanci na BBC.

Babban Marubucin Duniyar ya nemi Matasan Najeriya su yi kukan kura su fitar da ‘dan takara a zabe mai zuwa inda yace Dattawan kasar irin su za su mara masu baya don yana ganin lokacin da samari za su mulki kasar nan su yi gyara yayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel